Sabon shugabancin babbar jam'iyyar adawa na kasa a Najeriya PDP, ya bukaci jigo a jam'iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, da ya ci tuwon girma a matsayinsa na dattijon jam'iyya, kuma ya mayar da wukarsa kube, ya bayar da hadin kan da ya dace, don daidaita al'amuran jam'iyyar.
Sabon shugabancin jam'iyyar ta PDP na kasa, ya yi wannan kira ne bayan Sule Lamidon ya yi wata hira da sashen Hausa na BBC inda ya tabo batutuwa da dama ciki har da batun rikicin shugabancin jam'iyyar wanda har ya kai shi ga shigar da kara kotu.Shugabancin PDPn ya ce akwai gyara a wasu daga cikin bayanan da tsohon gwamnan na Jigawan ya yi.
Umar Sani, makusanci ne ga shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya shaidawa BBC cewa kamata ya yi tsohon gwamnan na Jigawa, ya yi hakuri ya mayar da komai ba komai ba.
Ya ce," Mai girma Sule Lamido, babba ne a jam'iyyar PDP, kuma yana cikin mutanen da ake da su a jam'iyyar to amma akwai bayanan da ya yi a hirarsa BBC wanda akwai gyara sosai a ciki."
Na farko da ya yi maganar shari'a inda ya ce mun saba ka'ida sannan munje yi babban taronmu na kasa har ma ya ce sam taron bai y iba, to ya kamata mutane su sani kotu bata bayar da umarnin dakatar da taro ba, abin da kotu ta ce a tantance shi sannan a bashi damar tsayawa takara, to mu kuma a tuni mun riga mun nemi kotun koli kan ta dakatar da gudanar da wannan hukunci , don haka um abin da muka yi yana bisa ka'ida."In ji shi.
Umar Sani, ya ce," A bangare guda kuma wata kotu a Ibadan ta bamu 'yanci na gudanar da babban taronmu, don haka bisa hukuncin kotun ta Ibadan muka gudanar da taronmu, kuma daya ce wai bamu da shugaba, to muna da shi tun da a babban taron mun zabi sabbin shugabanni."
Ya ce," A don haka muna kira ga Sule Lamido, a matsayinsa na babba, kuma a matsayin wanda suke da kyakkyawar fahimta da shi da Kabiru Tanimu Turaki, ya kamata ya ci girma musamman bisa la'akari da irin halin da jam'iyyarmu ke ciki."
" Ya kamata Sule Lamido ya yi hakuri ya dawo a dinke a ci gaba da wannan tafiya domin idan muka kasance a koyaushe muna kotu to ba zamu samu galaba." In ji Umar Sani.