Yansanda Sun Dakile Yunƙurin Satar Mutane A Abuja

Rundunar ƴansandan Abuja, babban birnin Najeriya ta daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane a ƙauyen Guto da ke ƙaramar hukumar Bwari.

Police
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce da tsakar daren da ya gabata ne jam'iansu suka samu rahotan wasu ƴan bindiga da suka kai talatin, sun shiga ƙauyen da nufin yin garkuwa da wani magidanci da iyalinsa.

Ta ce bayan samun rahoton, jami'ansu da ke yankin Bwari, da haɗin guiwar wasu jami'ai na musamman, sun yi gagagwar isa wurin, sai dai bayan ƴan bindigar sun hango su, sai suka buɗe wuta wanda ya sa ƴan sandan mayar da zazzafan martani, aka yi musayar wuta.

A cewar sanarwar, a yayin da ake musayar wutar, jami'an ƴan sandan sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga biyu, yayin da sauran suka tsere cikin dazukan da ke kusa.

Sai dai SP Josephine ta ce ɗaya daga cikin jami'an rundunar ya rasu bayan harbinsa da aka yi.

Sanarwar ta ƙara da cewa tuni kwamishinan ƴan sandan Abuja CP Miller Dantawaye ya aike da ƙarin jami'an tsaro domin ƙarfafa tsaro a yankin, ya kuma bayar da umurnin ƙaddamar da bincike domin gano ƴan bindigar.

Post a Comment

Previous Post Next Post