Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, a ranar Juma’a 26 ga Disamba, 2025, ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a fadarsa da ke Jihar Sokoto.
A cewar wani saƙo da aka wallafa a shafin Facebook na Hedikwatar Sojin Ƙasa ta Najeriya (HQ Nigerian Army) mai tabbaci da safiyar Asabar, ziyarar ta jaddada sabuwar ƙudurin Sojin Ƙasa na ƙarfafa alaƙar farar hula da soji, tare da bunƙasa haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya domin tallafa wa haɗin kan ƙasa, zaman lafiya da tsaro.A yayin ziyarar, Janar Shaibu ya sake tabbatar da aniyar Sojin Ƙasa na aiki kafaɗa da kafaɗa da shugabannin al’umma domin inganta kwanciyar hankali da zaman tare cikin lumana a faɗin ƙasar nan.
A nasa bangaren, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yabawa Sojin Ƙasa ta Najeriya kan sadaukarwa da jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin addu’ar samun ɗorewar nasara a kan ayyukanta na kundin tsarin mulki.