Wannan zauren zai tattauna ne kan waƙoƙin Hausa rubutattu da na baka, za a bita ne kan gudunmuwar da waƙoƙin ke bayarwa a fagen tattalin arziƙi da kuma yadda Bahaushe ke kallon waƙoƙinsa. Dr. Rabi'u Bashir shi ne zai zama jagoran wannan zauren inda zai ja ragamar sauran masu tattaunawar domin ganin an fitar da zare da abawa.
Dr. Rabi'u Bashir ya fito daga cikin zuriyar Alhaji Ɗambaba Ikara, a ƙaramar hukumar Ikara, Jihar Kaduna. Ya fara karatun addini a Makarantar Allo da ke gidan Alhaji Abdurakazak, Malamin Yara, a shekarar 1984. Daga nan ya halarci Central Primary School, Ikara daga 1985 zuwa 1991. Daga bisani aka shigar da shi Science Secondary School, Ikara, sannan daga baya ya kammala karatun sakandare a Government Secondary School, Ikara.
Ya ci gaba da karatu a Federal College of Education, Zaria daga 1999 zuwa 2002, inda ya samu Takardar Shaidar Koyarwa ta Ƙasa (NCE). A shekarar 2007 ya kammala digiri na farko (B.A Hausa) a jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria. Haka kuma, ya samu digiri na biyu (M.A African Languages) a 2014, sannan digirin digirgir (PhD African Literature- Hausa) a 2021, duk daga Sashen Harsunan Afirka da Al’adu jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.
Ya yi aiki da Kaduna State Primary Education Board kafin daga bisani ya yi murabus da kansa, inda ya koma aikin koyarwa a Kaduna State University.
Ya rubuta maƙalu na ilimi da dama a fannin da suka shafi adabi da al'adu. Masani ne kan waƙoƙin Hausa da kayan cikinsu.
2. Dr. Abdulrahman Aliyu yana da digirin farko (B.A), digiri na biyu (M.A), da digirin digirgir (Ph.D) a fannin Adabin Hausa daga Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina. A halin yanzu yana aiki da Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Ƙasa (National Assembly Service Commission), Abuja, inda yake bayar da gudunmawa a bincike da shawarwari da suka shafi manufofi da dokoki, musamman a fannoni na harshe, al’adu, da sadarwa. Sha’awarsa ta ilimi ta fi karkata ne ga Adabin Kwatance (Comparative Literature), inda ya maida hankali kan nazari da bincike na waƙoƙi, fina-finai, da fassara a cikin adabin Afirka da na duniya baki ɗaya. Ayyukansa na bincike suna duban yadda labaran gargajiyar Hausawa ke haɗuwa da sabbin salailan adabi, tare da mai da hankali kan yadda adabi da kafafen watsa labarai ke nuna ainihin al’adu, sauye-sauyen zamantakewa, da mu’amalar harsuna daban-daban. Ya gabatar da takardun bincike a tarukan ilimi da dama, kuma yana ci gaba da wallafa rubuce-rubucen ilimi da ke nazarin jigogi da salo a adabin Hausa da na kwatance. Bincikensa na yanzu ya maida hankali ne kan kwatancin adabin Hausa da sauran adabi na sassan Duniya.
3. An haifi Farfesa Aliyu a Kankara , jihar Katsina ran Juma'a, 20/12/1968. Ya halarci firamare kala-kala saboda yawan tashi da canjin aiki na mahaifi da mariƙinsa, kamar: LEA Kankara, LEA Islamiyya Daura, LEA Abakpa da LEA Saint Catholic church Tudunwada, dukansu a Kaduna, daga 1976 zuwa 1981. Ya halarci Kwalejin Gwamnati ta Katsina, 1981 zuwa 1986, da Kwalejin share fagen shiga Jami'a ta Zariya, 1986 zuwa 1990. Ya yi karatun digirin farko na nazarin Duwatsu da ma'adinai a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, 1990 zuwa 1994. Aliyu ya samu karatun digiri na biyu da na uku daga Jami'ar Bayero ta Kano da Jami'ar Fasaha ta Minna daga 1999 zuwa 2003, da kuma, daga 2007 zuwa 2014 inda a dukansu ya karanci sha'anin ma'adinai da sunadaransu. Ya koya a Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua daga 2007 zuwa 2012 a sashen ilimin Kasa da mihalli (Geography). A yanzu ya na koyarwa a Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsin-Ma, a sashen albarkatun fetur da ma'adinai daga 2012 zuwa yau. Ya wallafa littattafai na turanci da na Hausa da na wasan kwaikwayo har guda 46. Daga cikinsu akwai na Shata har guda uku. Ya ziyarci kasashe kamar su: Nijar, UAE (Daular Larabawa), Misra, Uganda, Habasha domin halartar tarurruka na kara ma juna Ilimi. Ya ziyarci Kasar Saudiyya cikin 2004. Ya na da aure da 'ya'ya.
Ya zama farfesa a fannin nazarin Duwatsu da ma'adinai a shekarar 2024. A fannin waƙa musamman ta baka shi rumbu ne ma'ajiyar kaya.
4. Hafiz Adamu Koza ɗalibi ne kuma malami mai jajircewa a fagen harshen Hausa, wanda ya yi karatun digirinsa na farko a jami'ar Umaru Musa Yar'adua, Katsina. Ya shahara wajen nazari, koyarwa da kuma rubuce-rubuce da suka shafi Hausa da Hausawa, inda yake amfani da ilimi da basira wajen bunƙasa harshen da adabin al’ummar Hausawa. Hafiz Adamu Koza marubucin waƙoƙin Hausa ne, wanda ke amfani da waƙa a matsayin hanyar isar da saƙonni masu ilmantarwa, tunatarwa da kuma gina al’umma. Waƙoƙinsa na tabo muhimman batutuwa da suka shafi al’adu, tarbiyya, rayuwar yau da kullum da kuma ƙalubalen zamani, ta yadda yake haɗa hikima da salo na zamani cikin rubutu. Haka kuma, fitaccen mai fafutuka a yanar gizo ne, inda yake amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaɗa ilimi, wayar da kai da kuma ƙarfafa matasa su rungumi harshen Hausa ta hanyar rubutu, karatu da kirkira. Wannan fafutuka tasa ta sanya ya zama ɗaya daga cikin muryoyin da ke taka rawar gani wajen kare martabar Hausa a duniyar zamani.
5. Badamasi Yusuf (BODMAS), haifaffen cikin garin Hadejia, Unguwar Majema. Ya fara karatunsa daga makarantar Muhammadiyya har zuwa karatun zamani. Yana da Diploma a Local Government Administration, sannan yana da Digiri (B.Sc) a Mass Communication. Haka kuma, yana da Professional Certificate da Professional Diploma kusan guda 36 a fannoni daban-daban. Makarancine Manazarci ne kuma marubuci, haka zalika marubucin waka. Shi ne Organizing Secretary a Kungiyar Marubuta ta kasa reshen JAHAR JIGAWA wato Association of Nigerian Authors Jigawa State chapter, shi ne Mataimakin Sakate a ƙungiyar Marubuta ta Hadejia Emirate Writers Association (HEWA) Ya Rubuta Littafai wasu da Hausa wasu da Turanci. A halin yanzu yana aiki a Jigawa State College of Remedial and Advanced Studies, Babura, inda yake rike da mukamin College Public Relations Officer (PRO).
