Dalilan Da Ke Haifar Sa Jar Hula Lokacin Bikin Kirsimeti

  • A lokutan bukukuwan Kirsimeti da mabiya addinin Kirista ke yi a faɗin duniya, kamar yadda ake ƙawata wurare da bishiyoyi masu lantarki haka ma za ka mutane na saka jar hula mai tulluwa da rastin fari a wuraren liyafa da taruka.

A wasu wurare kuma kamar manyan shaguna da ma'aikatu za ka ga an kakkafa hular a kusa da bishiyar lantarki ta Kirsimeti.

Ana dai kiran wannan hula da suna hular Santa.

Wannan ya saka jama'a da dama tambayar ko mene ne alaƙar wannan hula ja da Kirsimeti? Sannan wane ne shi Santa ɗin?

Santa wani mutum ne da ya yi suna a al'adar Kiristocin Yammaci wanda aka ce yana kai wa jama'a kyautuka da yammacin jajiberin Kirsimeti.

Sai dai kuma wani kaulin ya nuna cewa Santa Claus ya kasance mutumin da ya shahara a tatsuniyoyin ƙarni na huɗu da ke kira da Waliyyi Nicholas wanda mutum ne mai son ƙananan yara sannan kuma ya sanu da irin kirkinsa da yawan kyautuka.

Ana dai yawan kamanta Santa da fitaccen mutumin nan da Turawan Ingila suke kira da Father Chrismas inda kuma a yanzu haka ake kallon dukkannin su a mutum ɗaya - Father Chrismas shi ne Santa Claus.

Halayyar da aka sani ta Santa ita ce mutum ne mai ƙiba mai farin gemu inda wani lokaci ke sanye da gilashi sannan sanye da jar hula mai tulluwa da ratsin fari da kuma jar kwat da wando da takalmin ruwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post