Sojojin Isra'ila Ba Za Su Fice Gaba Daya Daga Gaza Ba - Israel Katz

Ministan tsaron Isra'ila ya ce sojojin Isra'ila ba za su fice baki daya daga zirin Gaza, a wani mataki da ake ganin zai janyo cikas a shirin Amurka na zaman lafiya a yankin

.

A jawabin da ya gabatar ga shugabannin yankunan da Yahudawa 'yan kama wuri zauna, Israel Katz, ya kara da cewa idan lokaci ya yi, za a samar da rundunar sojin Isra'ila maimakon a zaba cikin Falasdinawa da suka rasa muhallansu.

Wannan na nufin zama daram ga 'yan kama wuri zauna da ke wurin sama da shekaru 20. Firai minista Benyamin Netanyahu ya sha nanata fadada matsugunan yahudawa a zirin Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post