Fitaccen mawaƙin siyasa a arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya ce zai yi amfani da sarautarsa ta ƙasar Hausa domin haɗa kan mawaƙa tare da inganta sana'arsu.
Mawaƙin ya bayyana haka ne a zantawarsa da BBC Hausa, inda ya ce zai buɗe fadarsa ta sarauta, sannan zai naɗa hakimai da wakilansa da za su taimaka masa wajen gudanar da sarautar.A kwanakin baya ne Sarkin Daura Umar Faruq ya naɗa mawaƙin a matsayin Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa, a wani ƙasaitaccen biki da aka yi a fadar sarkin Daura da ke jihar Katsina.
A zantawarsa da BBC, Rarara ya ce, "na ji daɗi sosai da wannan sarauta ko muƙami. Kuma jin daɗin ya ta'allaƙa ne da yadda mutane suka karɓi naɗin," in ji shi.
Ya ce sarautar ta ƙara haska masa wasu abubuwa na rayuwa, musamman ganin yadda ya taso, da matakin da yake kai a yanzu na rayuwa.
"Ka ga ni almajiri ne, yayana ne ya saka ni a mota daga Kahutu aka kai ni jihar Kano domin karatun Qur'ani. Daga lokacin zuwa yanzu idan na duba rayuwata, sai in ga to me (ake buƙata) domi a kai maƙura?."
Ya ce a harkar waƙa da yake yi, yana ganin ya kai maƙura, domin a cewarsa, "a wannan rukunin da nake ciki, babu wani abu da ya ce wannan sarautar a gurina. Waƙa nake yi, kuma aka ce yau ni ne Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa baki ɗaya, gaskiya babu abin da ya wuce wannan a wajena. Babu wani biki da ya fi wanan."