Ƙungiyar raya tattalin arziki na ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta buɗe taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar a Abuja babban birnin Najeriya yau Lahadi.
Taron karo na 68 na gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, inda za su tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi yankin"Taron zai shirya muhawara kan makomar ƙungiyar, da abubuwan da yankin zai saka a gaba cikinsu har da kwanciyar hankali a harkokin siyasa, da hadin gwiwa kan tsaro, da kuma faɗaɗa harkokin tattalin arziki," kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wurin buɗe taron, wanda ke zuwa a daidai lokacin da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi ke zafafa hare-hare a ƙasashen Najeriya da Mali da Burkina Faso da Nijar.
Sai dai Nijar da Mali da Burkina Faso sun fita daga ƙungiyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen.