Wasu Yan Najeriya Sun Yi Kira Da a Sauke Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle

A Najeriya, jama'a na ci gaba da bayyana damuwa game da yawaitar zargin da ake yi wa karamin ministan tsaro na kasar, Bello Matawalle, cewa yana da alaka mai karfi da 'yan bindiga, kuma yana taimaka masu.

Har ma ana ta yi masa matsin lamba a kan ya sauka daga mukaminsa, a gudanar da cikakken bincike kansa don ya wanke kansa.

Sakamakon haka ma wasu lauyoyi masu zaman kansu sun bayyana aniyar shigar da kara kotu, game da zarge-zargen da ake yi wa karamin ministan.

Sai dai ministan ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, da cewa siyasa ce wadda ba yau aka fara ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post