Fulani sun koka kan yadda yan sa-kai ke hana su sakat da ci masu zarafi a jihar Zamfara

Kungiyoyin Fulani a yankin arewacin Najeriya na nuna damuwa game da abin da suka kira jama'u da ake yi wa al'ummarsu sanadiyyar matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin.

Kungiyar Fulani

Suna zargin cewa ana zaluntar ƴan ƙabilar ta Fulani wadanda ba su, ba su gani ba ta hanyar cin mutuncinsu da kona masu rugage da kwashewa ko ma karkashe masu dabbobi, baya ga kisan gilla da ake yi masu a wurare da dama.

Hakan kuwa yana hana su walwala da shiga garuruwa, da kasuwanni da cudanya da sauran jama'a.

Ƙorafi na baya-baya nan da al'ummar Fulanin ke yi game da irin tsangwamar da suke kukan ana yi musu ya fito ne daga jihar Zamfara inda wani magidanci Bafulatani a ƙaramar hukumar Gumi, ya ce Fulani sun zama masu fargabar fitowa ko yin tafiya a kan tituna saboda hare-haren ‘yan sa-kai ba don komai ba, sai domin kasancewarsu Fulani.

"Yanzu haka da nake magana, hanyarmu nan daga Gumi, Bafulatani bai isa ya wuce ba saboda matsalar ƴan sa-kai, kama mu suke yi su kashe."

Lokacin da aka tambaye shi ko wasu ɓata-gari ne ke aikata hakan, sai ya ce: "Ba yan ɓata gari ne ke aikata hakan ba, ƴan sa-kai ne ɗauke da makamai," in ji shi.

Da aka tambaye shi ko yana ganin zargin wasu Fulani ne da ke kai hare-hare ne ya jawo hakan, sai ya ce "Cikin Fulanin, ba kowa ba ne ɗan ta'adda.

Zamfara da sauran jihohin arewa maso yammacin ƙasar na fama da matsalar ƴan bindiga masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Ana zargin cewa Fulani ne waɗanda suka fi yawa cikin ƴan bindigar da ke kai hare-haren kan al'umma.

Sai dai wani abuda masana ke ganin yana iza wutar rikicin shi ne ayyukan ƴan sa-kai da ke kare ƙauyukan da ake kai wa hari, inda a wasu lokuta ake zargin cewa sukan dauki matakai ba tare da bin ƙa'idojin doka ba sanadiyyar rashin ƙwarewa.

A martaninta, gwamnatin jihar Zamfara dai ta yi Allawadai da aukuwar irin wannan lamari kuma ta lashi takobin magance matsalar, a cewar Mustapha Jafaru Kaura, mai bayar da shawara kan harkokin yaɗa labarai ga gwamnan jihar Dauda Lawal.

"Shi wannan lamari na ƴan sa-kai da ke kashe Fulani a Zamfara, gwamnatin jihar ba ta tare da duk wani nau'i na cin zali da cin zarafi ko tsangwama kuma ba za ta lamunci irin waɗannan abubuwan ba."

"Za a haɗa kwamiti ba da dadewa ba domin gudanar da bincike da kuma hukunta masu laifi."

Jihar Zamfara ta kafa rundunar tsaro ta Askarawa, wadda ke taimakawa bayan sojojin gwamnatin Najeriya da ke aiki a yankin.

Sai dai a baya an zargi Askarawan da wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukansu, inda har gwamnatin jihar ta ce za ta gudanar da bincike a kai.

Post a Comment

Previous Post Next Post