NACETEM Na Sahun Gaba Wajen Tsara Manufofin Fasahar AI a Najeriya — Dr. Odusanya

Darakta Janar na Cibiyar Gudanar da Fasaha ta Kasa (NACETEM), Dr. Olushola Odusanya, ya bayyana cewa cibiyar na taka rawar gani a sahun gaba wajen tsara manufofin fasahar kera kwakwalwa (Artificial Intelligence - AI) a Najeriya, domin tabbatar da cewa kasar ta shirya tsaf ga sauye-sauyen tattalin arzikin zamani na duniya.

Dr. Odusanya ya jaddada cewa makomar Najeriya ba za ta ginu akan tattauna matsaloli ba, muddin dai za a yi amfani da yaren "mafita" wanda kirkire-kirkire ke tunkara.

Yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya sanar da manyan sauye-sauyen da ke mayar da hukumar zuwa wata kashin baya ta fuskar Kimiyya, Fasaha, da Kirkire-kirkire (STI), Darakta Janar din ya bayyana cewa: "Muna jagorantar tattaunawa kan manufofin fasahar AI a Najeriya domin tabbatar da cewa kasarmu ta kasance cikin shiri ga kalubalen gobe."

Muhimman Nasarori da Sauye-sauye

Shugaban ya bayyana cewa NACETEM ta riga ta fara amfani da tsarin dijital a dukkan ayyukanta, ciki har da tsarin karin girman ma'aikata. Wannan mataki a cewarsa, ya taimaka wajen:

  • Rage Kashe Kudade: Ta hanyar yanke al'adun balaguron da ba su zama dole ba.

  • Gaskiya da Adalci: Samar da tsarin gudanarwa da kowa zai iya amincewa da shi.

Kalubale da Hada-aka

Duk da cewa ya amince da akwai kalubale kamar karancin kudade da rishin ababen more rayuwa, Dr. Odusanya ya nuna cewa sun fadada hadin gwiwa da jami'o'i, cibiyoyin bincike, masana'antu, da bangarorin gwamnati. Haka kuma, cibiyar ta kara kaimi wajen bayar da horo na kwararru da karatun digiri na biyu da na uku domin karfafa gwiwar kwararru a fannin kimiyya da fasaha.

A cewarsa, irin wannan hadin gwiwa za ta bude kofofin bincike na hadin gwiwa, horarwa ta musamman, da kuma amfani da fasaha wajen garambawul din da zai karfafa hukumomi da kyautata shugabanci a kasa baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post