shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, Ahmed Farouk.ya ajiye aikinsa.
Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya ta ce tuni shugaba Tinubu ya aike da sunan mutumin da zai gaji Farouk Ahmed.Wannan dai na zuwa ne kwana uku bayan da shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Aliko Dangote ya yi zargin cewa Farouk Ahmed na biya wa ƴaƴansa guda huɗu kuɗin makaranta a Switzerland da suka kai dala miliyan biyar.
Tuni dai hukumar yaƙi da almundahana ta Najeriya ICPC ta ce za ta yi bincike kan zargin da shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi wa shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, Ahmed Farouk.