A daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara kan zargin ana cin zarafi ko kuma yi wa Kiristocin Najeriya kisan kiyashi, musamman a arewacin ƙasar, gwamnatin Amurka ta ɗauki matakin hana wasu ƴan Najeriyar shiga ƙasarta.
Wata sanarwa da fadar gwamnatin Amurka ta fitar a ranar Talata ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da za a taƙaita wa mutanenta shiga Amurka.Wannan na cikin matakin da ƙasar ta Amurka ta ɗauka wajen hana al'umma daga ƙasashe da dama shiga cikinta bisa dalilai daban-daban.
A kwanakin baya Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar shiga Najeriya da sojoji, inda ya ce zai je ne domin yaƙi da ta'addanci matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta ɗauki matakin gaggawa ba.