Gwamnatin Somaliya ta yi kakkausar suka tare da Allah-wadai da matakin da Isra’ila ta ɗauka na amincewa da yankin Somaliland a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, tana mai bayyana hakan a matsayin “mamaya tsirara da tauye ikon ƙasa.”
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Somaliya ta fitar, gwamnatin ta ce matakin Isra’ila ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjejeniyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda ke tabbatar da cikakken ikon Somaliya a kan dukkan yankunanta, ciki har da Somaliland.
Somaliya ta jaddada cewa Somaliland wani ɓangare ne na ƙasar Somaliya, kuma duk wani yunƙuri na amincewa da yankin a matsayin ƙasa dabam na iya ƙara tayar da rikici da rashin zaman lafiya a yankin Kahon Afirka. Ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su ƙi amincewa da matakin Isra’ila.
A gefe guda kuma, hukumomin Isra’ila ba su fitar da cikakken bayani kan martanin Somaliya ba, yayin da wasu ƙasashen duniya ke nuna damuwa kan yiwuwar wannan mataki ya haifar da sabon rikici na siyasa da tsaro a yankin.