Ana raderadin Yanbindiga daga jihar Zamfara Sun dasa nakiya a kan hanyar Dansadau da ke cikin karamar Hukumar Maru. A Arewa maso yammacin Najeriya. Babbar hanya ce wadda ta hada yankin da karamar hukumar Gusau.
Hunkula sun tashi a yankunan da abun ya faru da ma sauran sassa jihar baki daya. Ganin yadda ƴan ta'addar suka fara amfani da irin wannan makami.
Mutanen yankin sun nemi Agajin masu rike da madahun iko na a kai musu Agajin gaggawa don dakile ire-iren wadannan hare-haren nan gaba.