Kanar (Farfesa) Engr. Abubakar Surajo Imam fitaccen jarumi ne a rundunar sojin Nijeriya, kuma shi ne sojan da ke kan aiki na farko da ya kai matsayin Farfesa. Ƙwararre ne a Injiniyan Mechatronics, yana koyarwa Nigerian Defence Academy (NDA), inda yake jagorantar Sashen Mechatronics Engineering da kuma Cibiyar Kirkire-kirkire.
Asalinsa ɗan Jihar Katsina ne, aikinsa ya haɗa hidimar soja da ilimi a matakin ƙoli, inda ya samu digiri na PhD daga Birtaniya, tare da ƙirƙira da haɓaka sabbin hanyoyin fasaha da suka taimaka wa rundunar soji. Hakan ya sanya ya taka rawar gani sosai a injiniyan soja da binciken kimiyya.
*Haihuwa da Ilimi*
An haife shi ranar 22 ga Yuni, 1976, a Kankia, Jihar Katsina, Nijeriya. Ya yi Firamare: Sultan Bello Primary School, Kaduna (1982–1987) sannan Sakandare: Government College Katsina (1988–1991). Ya sau digiri na Farko a fannin Injiniyan Na’ura a Jami'ar Bayero Kano (2001). Ya yi Digiri na biyu M.Sc. (2009) da PhD (2014) a Mechatronics da Robotics, Newcastle University, Birtaniya.
*Aikin Soji*
Ya shiga rundunar Nigerian Army ta hanyar Short Service Combatant Course 32, inda aka tura shi Corps of Electrical & Mechanical Engineers (EME). Daga baya aka sauya shi zuwa Regular Commission. Ya yi aiki a sassa daban-daban na EME, ciki har da 1 Base Workshop da Hedkwatar EME Corps
Farfesan Soja na Farko: Ya zama sojan Nijeriya na farko da ke kan aiki da ya kai matsayin Farfesa, tun daga Oktoba 2022. Ya jagoranci Sashen Mechatronics Engineering da Cibiyar Kirkire-kirkire a NDA. Yana gudanar da bincike tare da cibiyoyi kamar Air Force Institute of Technology (AFIT) da Ahmadu Bello University (ABU).
Ya ƙera tare da aiwatar da sabbin hanyoyin fasaha da dama, masu amfani ga soja da farar hula, ta hanyar haɗa injiniyan na’ura, injiniyan lantarki, da kimiyyar kwamfuta. Ya wallafa maƙalu da takardun ilimi da dama a duniya.
A karon farko zai kasance tare da wannan taron domin fayace yadda marubuta ya kamata su yi amfani da fasahar AI a rubutunsu.
