Sabon shugabancin babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ya yi watsi da wa'adin kwanaki goma da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, ya bayar na a rushe shugabancin jam'iyyar.
Tsohon gwamnan dai ya buƙaci jam'iyyar PDP ta warware rikicin cikin gida da ya yi mata katutu wanda ya haɗa da rushe babban taronta da ta gudanar a birnin Ibadan, da kuma abin da aka cimma.A cewar shugabancin jam'iyyar ta PDP, bai kamata a ce tsohon gwamnan na Jigawa, da ake yi wa kallon dattijo a jam'iyyar da ya ba da gudummawa wajen ci gabanta, ya dawo yana neman cindunduniyarta ba, don haka akwai bukatar ya mayar da wukarsa cikin kube, ya zo a sasanta.
Alhaji Umar Sani, jigo ne a jam'iyyar ta PDP, kuma mai taimakawa shugaban jama'iyyar na kasa Tanimu Turaki, ya shaida wa BBC cewa, a matsayinsa na babba kuma wanda ya san siyasa kana ya san yadda ake tafiyar da jam'iyya, to ya ajiye komai ya dawo ayi tafiya tare.
Ya ce," A yanzu jam'iyyarmu ta PDP, bata bukatar komai sai hadin kai duk wasu rigingimu ya kamata a jinginesu don a samu aka kai ga gaci."
Abin da Sule Lamido da wasu ke so jam'iyya ta yi ba zai yiwu ba domin duk abin da ya kamata ayi an yi don haka babu mayar da hannun agogo baya."In ji shi.
Alhaji Umar Sani,ya ce," Duk abin da ya kamata mu yi kai hatta shi shugaban jam'iyya sai da ya nemi su gana da Sule Lamido don a fahimci juna amma hakan bai yiwu ba, don haka babu wani da za ayi kuma."
To sai dai duk da wannan kira da jagororin jam'iyyar ta PDP ke yi, wasu makusantan tsohon gwamnan na Jigawa Sule Lamido, sun ce ko a jikinsu, domin tun farko, rashin bin ka'ida ne ya sa suka ja daga.