Yadda Taron Karramawa Gwarazan Hikayata Na 2025 Ya Wakana

A ranar Alhamis 11 ga watan Disamba ne aka gudanar da bikin karrama gwarazan gasar gajerun labarai ta Hikayata ta shekarar 2025.

A wajen taron na bana, tsohon shugaban sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh, wanda shi ne ya jagoranci assasa gasar, ya ce an ƙirƙiri gasar ne domin karfafa guiwar marubuta mata tare da fito da fasaharsu.

Ya ce yana alfahari tare da farin cikin ganin wannan shekarar da gasar ta cika shekara 10, sannan ya ce labaran da ake turowa za su yi kyau wajen shirya fina-finai, sannan ya ce tuni an nazarci labarai da nasarorin gasar a jami'o'i.

A wajen taron, an tafka muhawara kan muhimmancin ilimin mata, inda Farfesa Abdullah Uba Adamu da Rahama Abdulmajid da Dr Ibrahim Sheme da Fatima Zahra Umar suka tattauna kan maudu'in.

Post a Comment

Previous Post Next Post