Sojoji Sun Kashe Na Hannun Damar Turji

Sojojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Kallamu, wanda na hannun damar Turji ne a ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.

Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ce ta ruwaito daga wata majiya cewa an kashe ɗanbindigar ne a ranar Laraba, inda ta ce an samu nasarar kashe Kallamu ne tare da taimakon ƴan sa kai.

Kallamu ɗan asalin garin Garin-Idi ne da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, inda rahotanni suka ce Kallamu ya tsira daga wasu hare-haren sojoji a baya, inda aka ce ya tsere zuwa jihar Kogi.

Jihar Sokoto ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro, duk da irin nasarorin da sojojin Najeriya suke cewa suna samu.

Post a Comment

Previous Post Next Post