Yayin da ake cika shekara 60 da juyin mulkin soji na farko a Najeriya, BBC ta kai ziyara inda aka binne gawar mutum mafi girman muƙami da aka kashe a lokacin juyin mulkin.
Abubakar Tafawa Ɓalewa shi ne Firaiministan Najeriya na wancan lokaci, kuma yana cikin waɗanda sojojin suka hallaka a shekarar 1966, baya ga Firimiyan jihar Arewa da na Yamma da kuma manyan sojoji da masu riƙe da muƙaman gwamnati.Shi ne juyin mulkin da ya kawo ƙarshen jamhuriya ta farko a Najeriya, wadda ta ƙunshi fitattun mutane da suka yi fafutikar samun ƴancin kan ƙasar.
An binne marigayin ne a garin Bauchi da ke jiharsa ta asali a arewa maso gabashin Najeriya