Gajeren Zaman Xabi Alonso a Real Madrid

 Zaman Xabi Alonso a matsayin kocin Real Madrid bai ɗauki lokaci mai tsawo ba, amma ya kasance cike da matsaloli, sakamako marasa daɗi da kuma rikice-rikicen cikin gida da suka janyo cece-kuce a duniyar ƙwallon ƙafa.

Xabi Alonso

A gasar Champions League, Real Madrid ƙarƙashin Alonso ta ƙare a matsayi na 7, sakamako da ya gaza abin da magoya baya da shugabanci ke tsammani daga ƙungiyar da ta saba mamaye Turai.

Haka kuma, Madrid ta sha kashi a hannun Barcelona a wasan Supercopa, abin da ya ƙara tayar da hankalin magoya baya, musamman ganin yadda abokiyar hamayya ta fi Madrid ƙarfi da tsari a wancan lokaci.

Rahotanni sun kuma nuna cewa Alonso ya shiga rikici da Vinícius Júnior, wanda ake cewa rashin jituwa tsakaninsu kan salon wasa da umarnin koci ya shafi yanayin ɗakin sauya kaya.

Masana kwallon ƙafa na ganin cewa haɗuwar matsin lamba, rashin nasarori, da rikicin ‘yan wasa ne suka sa gajeren zaman Xabi Alonso a Real Madrid ya zama ɗaya daga cikin lokutan da aka fi samun hayaniya a tarihin kulob ɗin.

Post a Comment

Previous Post Next Post