Aƙalla Palasɗinawa uku ne suka rasa rayukansu bayan wani hari da sojojin Isra’ila suka kai kan sansanin tantuna a Zirin Gaza, inda fararen hula ke samun mafaka daga hare-haren da ake ci gaba da kaiwa yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya afku ne da daddare, inda jiragen yaƙin Isra’ila suka jefa makamai kan tantunan da ke cike da mata da yara da kuma tsofaffi. Shaidu sun ce harin ya janyo tashin gobara tare da raunata wasu mutane da dama.
Ma’aikatan agaji sun ce tantunan da aka kai wa hari na dauke da iyalan da suka riga suka rasa gidajensu sakamakon hare-haren baya. Sun bayyana lamarin a matsayin mummunan keta dokokin kare fararen hula a lokacin rikici.
A nasa bangaren, Isra’ila ba ta bayar da cikakken bayani kan harin ba, sai dai ta sha bayyana cewa tana kai hare-hare ne kan wuraren da take zargin mayakan Hamas na amfani da su. Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam na ci gaba da sukar irin wadannan hare-hare.
Yayin da rikicin ke ci gaba, al’ummar Gaza na fuskantar mawuyacin hali, inda ake fama da karancin abinci, ruwa da magunguna, tare da karuwar asarar rayuka a kullum.