Jiragen Yakin China, Rasha da Iran Sun Isa Afirka ta Kudu Don Atisayen Soja

 Jiragen ruwan yaƙi na ƙasashen China, Rasha da Iran sun isa Afirka ta Kudu domin gudanar da atsayen soji na haɗin gwiwa a tekun kudancin ƙasar. Atisayen na daga cikin ƙoƙarin ƙasashen uku na ƙarfafa haɗin kai a fannin tsaro da soja.

Jiragen ruwan yaƙi

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana cewa atisayen zai gudana ne a tekun Cape Town, inda sojojin ruwan ƙasashen za su yi atisaye kan dabarun tsaron teku, ceton jiragen ruwa, da kuma musayar ƙwarewa a fagen soja. Hukumomi sun ce atisayen ba ya nufin barazana ga wata ƙasa.

Wannan hadin gwiwa na soja ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a siyasar duniya, musamman tsakanin ƙasashen Yamma da wasu manyan ƙasashen duniya. Masana harkokin tsaro na ganin atisayen na nuni da ƙoƙarin China, Rasha da Iran na nuna ƙarfinsu a fagen kasa da kasa.

Sai dai wasu ƙasashe da ƙungiyoyi sun nuna damuwa kan wannan atisayen, suna cewa hakan na iya ƙara rura wutar rikici da rashin jituwa a duniya. Duk da haka, Afirka ta Kudu ta jaddada cewa ƙasar na bin manufar ƙawancen kowa da kowa, ba tare da fifita wani bangare ba.

Ana sa ran atisayen zai ɗauki kwanaki da dama, inda sojojin ruwan ƙasashen za su yi ayyuka daban-daban a teku. Wannan na ɗaya daga cikin jerin atisayen soja da ƙasashen uku ke yi a sassa daban-daban na duniya a ‘yan shekarun nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post