Sojojin Siriya sun yi gargaɗin cewa za su sake ƙaddamar da sabbin hare-hare a birnin Aleppo, sa'o'i bayan mayaƙan Ƙurɗawa sun yi watsi da sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
An umarci fararen hula su fice daga yankin Sheikh Maksoud da ke birnin.An riƙa samun arangama mai zafi cikin makon nan tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan Ƙurɗawa ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar SDF.
Ƙungiyar ta masu tayar da ƙayar baya ta ƙi janyewa daga wuraren da ta mamaye, kamar yadda sharuɗan yarjejeniyar suka tanada.
Ɓangarorin biyu na samun saɓani kan haɗe ƙungiyar mayaƙan cikin dakarun gwamnati.