Rasha ta harba wani makami mai linzami mai karfin gaske birnin Lviv da ke yammacin Ukraine, a cikin jerin hare-hare ta sama da ta yi a ƙasar cikin daren jiya.
An kai hare-haren a birane da dama, duk da dai an kaƙƙaɓo wasu makaman bayan samun gargaɗin ana shirya kai harin.Ukraine ta ce hare-haren da aka kai kusa da yankunan Tarayyar Turai da ƙungiyar NATO babbar barazana ce ga tsaron ƙasashen Turai.
Jamus ta yi Alla-wadai da hare-haren, yayin da babbar jami'ar diflomasiyya ta Tarayyar Turai, Kaja Kallas ta ce hare-haren na nuna lamarin na ci gaba da ta'azzara, kuma ya kasance kamar wani gargaɗi ne.
Aƙalla mutum huɗu ne suka mutu a Kyiv, kuma hare-haren sun shafi ofishin jakadancin Qatar.