Tawagar Super Eagles ta tafi Marakech Domin Buga Wasan Kwata-Fainal

Ƴan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya sun tafi birnin Marakech domin buga wasan kwata-fainal da za su fafata da tawagar ƙasar Aljeriya.

Da farko dai an samun rahotannin da ke cewa ƴan wasan sun yi barazanar ƙin buga wasan matuƙar ba a biya su kuɗaɗen alawus ɗinsu ba.

Sai daga baya shugaban hukumar wasanni ta Najeriya, Shehu Dikko ya ce an shawo kan matsalar, sannan jim kaɗan aka ga ƴan wasan suna hawa jirgi za su tafi birnin da za a buga wasan.

Post a Comment

Previous Post Next Post