Masana Sun Ce Daukar Maduro Ya Saba Wa Ka’ida

 Masana harkokin doka da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa ƙwace shugaban Venezuela Nicolás Maduro da sojojin Amurka ya saba wa dokokin duniya, duk da cewa Amurka ta kai shi gaban kotun tarayya a New York kan zargin laifuka da suka haɗa da fataucin ƙwayoyi. 

Maduro

A cewar masana, babu amincewar gwamnatin Venezuela ko izinin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ya ba da izinin amfani da ƙarfin soja wajen kama shugaban ƙasa a gida. Wannan ya sa yawancin kwararru ke kallon aikin a matsayin cin zarafin ‘yancin ƙasar da tauye ka’idojin dokar ƙasa da ƙasa.

Maduro, wanda Amurka ta tuhume shi a shekarar 2020 kan zargin haɗin guiwa da ƙungiyoyin fataucin ƙwayoyi, ya bayyana a kotu a New York inda ya musanta laifukan, yana mai cewa an sace shi daga Caracas. 

Masana sun yi gargadi cewa kamawa da kuma kwace shugaban ƙasa ba tare da amincewar ƙasar sa ba na iya zama wani misali mara kyau da zai ƙara lalata tsarin dokokin ƙasa da ƙasa, inda a ka’ida shugaban ƙasa na da kariya na musamman (sovereign immunity) daga kamawa daga wata ƙasa. 

Duk da haka, Amurka na ƙoƙarin kallon lamarin a matsayin aikin hukuma na yaki da laifuka, ba a matsayin yaki da ƙasar Venezuela ba. Wannan ya sa akwai sabani tsakanin gwamnatoci, masana doka da ƙungiyoyi na duniya kan halaccin ɗaukar matakin. 

Post a Comment

Previous Post Next Post