KANU: “FANARETI FANARETI NE” BAYAN SUPER EAGLES TA SHA KASHI A HANNUN MOROCCO A WASAN SEMI-FINAL NA AFCON

Tsohon ɗan wasan Arsenal, Nwankwo Kanu, ya bayyana a daren ranar Alhamis cewa “fanareti fanareti ne” bayan Super Eagles ta Nijeriya ta sha kashi a hannun Morocco a wasan kusa da na ƙarshe na gasar AFCON da aka fafata a ranar Laraba.

KANU
Kanu, wanda ya halarci wasan a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat, domin tallafa wa tawagar da Eric Chelle ke jagoranta a karawar da Atlas Lions (Morocco), ya ce ‘yan wasan Nijeriya sun yi ƙoƙari matuƙa duk da rashin nasarar da suka fuskanta.

Za a tuna cewa Nijeriya ta sha kashi da ci 4–2 a bugun fanareti, bayan an tashi wasan babu ci babu cici (0–0) a lokacin ƙarewar wasa da ƙarin lokaci a wasan kusa da na ƙarshe.

‘Yan wasa irin su Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi sun kasa cin nasarar jefa bugun fanaretinsu, lamarin da ya taimaka wajen faduwar Super Eagles a hannun Morocco.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Kanu ya nuna farin cikinsa da haɗuwa da tsohon kocinsa, Arsène Wenger, inda ya wallafa hotonsu tare a filin wasan.

Kanu ya rubuta cewa: “Abin farin ciki ne koyaushe ganin Farfesa Arsène Wenger. Fanareti fanareti ne. Ina taya Super Eagles murna. Kun yi gwagwarmaya mai kyau.”

Post a Comment

Previous Post Next Post