Uwar ɗaya daga cikin ya’yansa Elon Musk ta shigar da ƙara kan kamfanin AI da Musk ke da alhakin shi, inda take zargin cewa an yi amfani da fasahar Grok wajen ƙirƙirar hotunan deepfake na batsa da suka yi mata ɓarna ba tare da izini ba.
A cikin ƙarar da ta shigar a gaban wata kotu, matar ta ce an yi amfani da sunanta da hotunanta cikin waɗannan deepfake ba tare da ta bayar da izini ba, lamarin da ya jawo lahani ga mutunci da walwalarta, har ya kai ga matsalolin tunani da na zamantakewa.
Deepfake na nufin hotuna ko bidiyo da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar basirar wucin gadi (AI) wanda yake nuna wani a matsayin mutum daban ko kuma a yanayi da bai dace ba. A wannan lamari, an ce hotunan sun haɗa da abubuwan da ke da alaƙa da batsa, abin da ya sa matar ta ji ɓata rayuwa da tsangwama daga jama’a.
Masu lauyoyi sun bayyana cewa kamfanin AI, wanda ke haɓaka Grok, ya gaza daukar matakan da suka kamata wajen ƙarfafa tsaro da kiyaye haƙƙoƙin masu amfani, inda hakan ya bai wa wasu damar amfani da fasahar wajen cutar da wasu.
A halin da ake ciki, har yanzu kamfanin ba yaɓa yin wani ɗan tsokaci kai tsaye kan ƙarar ba, sai dai masana harkar fasaha sun nuna damuwa kan yadda fasahar AI zata iya kawo ƙalubale ga sirri da haƙƙin mutum idan ba a tsara dokoki da ƙa’idoji masu ƙarfi ba.