Kotu ta Bayar da Umarnin Dakatar da Yunkurin Tsige Fubara

Wata babbar kotun Rivers ta bayar da wani umarnin wucin-gadi na dakatar da yunƙurin tsige gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Nma-Odu.

Cikin hukuncin da ta bayar a birnin Fatakwal, kotun ta dakatar da kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule da wasu mutane da ake ƙara - ciki har da akawun majalisar da alƙalin alƙalan jihar - daga yunƙurin tsige gwamnan, kamar yadda Gudan talbijin na Channels ya ruwaito.

Haka kuma kotun ta bayar da wani keɓantaccen umarni na hana alƙalin alkalan jihar, Mai Shari'a Simeon Chibuzor-Amadi, karɓar wani ƙorafi ko miƙa shi ko kuma duba wata buƙata ko shawara da ta jiɓanci batun tsige gwamnan daga majalisar dokokin jihar, har zuwa nan da kwana bakwai, kamar yadda hukuncin kotun ya nuna.

Gwamnan jihar da mataimakiyarsa ne suka shigar da ƙarar daban-daban a gaban kotun, don neman wannan buƙata.

Jihar Ribas dai na fama da rikicin siyasa tun bayan zaɓen 2023, lamarin da ya kai ga Shugaba Tinubu dakatar da gwamnan na tsawon wata shida a shekarar da ta gabata.

Post a Comment

Previous Post Next Post