Jagoran Addinin Iran ya Amince da kisan Bubban masu zanga-zanga

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, A karon farko ya fito fili ya amince da cewa an kashe dubban mutane, wasu ta hanyar rashin mutuntaka da rashin tausayi, yayin zanga-zangar baya-bayan nan.

A wani jawabi da ya yi a ranar Asabar, ya zargi Amurka da Donald Trump da alhakin kitsa zanga-zangar da ta janyo "ɓarna da kuma batanci" a ƙasarsa.

Shugaban Amurka ya buƙaci masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Iran da su ci gaba da yin zanga-zanga, ya kuma yi barazanar ɗaukar matakin soji idan jami'an tsaro suka kashe su.

Har yanzu daiTrump bai mayar da martani ga shugaban na Iran ba kuma BBC ta tuntubi fadar White House domin jin ta bakinsa.

Zanga-zangar da aka yi a Iran ta yi sanadin mutuwar mutane 3,090, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Iran (HRANA), a Amurka, a tarzomar da ta faro kan tattalin arziki a ranar 28 ga Disamba.

Tun daga wannan lokaci zanga-zangar ta rikiɗe zuwa kiraye-kirayen kawo ƙarshen mulkin shugaban ƙasar Iran.

Gwamnatin Iran ta bayyana zanga-zangar a matsayin tashin hankalin da maƙiyan Iran ke marawa baya.

Post a Comment

Previous Post Next Post