Wasu da ake zargin ƴan daba ne sun kashe wata matar aure da ƴaƴanta, a gidansu da sanyin safiyar ranar Asabar a jihar Kano.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta ce mummunan lamarin dai ya faru ne a lokacin wasu da ba a tabbatar da ko su waye ba suka afkawa Fatima Abubakar mai shekara 35 da ƴaƴanta shida, a gidansu da ke Dorayi Charanchi Quarters da muggan makamai inda suka ji masu munanan raunuka.Sanarwar dai ta ƙara da cewa, An kwashe waɗanda lamarin ya shafa kuma aka garzaya da su asibitin Murtala da ke Kano, inda aka tabbatar da mutuwarsu.
Yaiyinda ta ke mi\ka ta'aziyarta ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa, rudunar ƴansandan jihar ta bayar da tabbcin gudanar da cikakken bincike kan lamarin da niyan zaƙulo waɗanda ke da hannu a ciki.