Ƴan Denmark na zanga-zangar adawa da ƙwace Greenland

Dubban mutane sun taru a wajen birnin Copenhagen na ƙasar Denark domin nuna adawarsu kan matakin Shugaba Trump na ƙwace iko da yankin Greenland, mallakin ƙasar.

Masu zanga-zangar na riƙe ta kwalaye masu ɗauke da saƙonnin da ke cewa ''Ka haƙura da Greenland'', ''Greenland na ƴan yankin ne''

Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da wata tawagar ƴansiyasar Amurka ke ziyara a yankin, inda shugaban tawagar Sanata Chris Coons na jam'iyyar Dimokrats ya bayyana matakin na Trump a matsayin wanda bai ''dace ba''.

A ranar Juma'a ne Mista Trump ya ce zai iya sanya haraji kan ƙasashen da suka nuna adawa da shirin nasa.

Haka kuma shugaban na Amurka bai musanta ƙwace yankin ta ƙarfin tsiya ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post