Liverpool ta zama ƙungiyar Premier da ta fi samun kuɗi karo na farko, a cewar kamfanin haraji na Deloitte.
Ƙungiyar ta lashe gasar Premier karo na 20 a bara, inda ta samu kuɗaɗen shiga da suka kai yuro miliyan 836 - wanda ya zarta na kowace ƙungiyar kwallon kafa a Ingila.Yayin da Manchester United kuma ta faɗi zuwa mataki na ƙasa, a cewar Deloitte Football Money League.
Real Madrid ta sake ɗare wa saman jerin ƙungiyoyin da suka fi samun kuɗi a duniya, inda ta samu kuɗin shiga yuro biliyan 1.2, duk da cewa ba ta lashe Champions League ko La Liga ba a bara, sai kuma ƙungiyoyin birnin Manchester da suka rikito daga saman jerin zuwa ƙasa.