Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rugujewar tumbin shara (landfill) a ƙasar Philippines ya ƙaru zuwa mutane huɗu, yayin da rahotanni ke cewa har yanzu akwai mutane da dama da suka maƙale a ƙarƙashin tarin shara.
Lamarin ya faru ne bayan wani ɓangare na babban tumbin shara ya rufta, inda ya binne gidaje da ke kusa da wurin. Shaidun gani da ido sun ce rugujewar ta zo ne kwatsam, lamarin da ya sa mutane ba su samu damar tserewa ba.Jami’an ceto da na gaggawa na ci gaba da aikin tonon ceto dare da rana, duk da ƙalubalen da suke fuskanta sakamakon wari, laka da kuma haɗarin sake rushewa. Sun ce ana fargabar yawan waɗanda suka makale ya fi adadin da ake zato tun farko.
Hukumomi sun bayyana cewa yawancin mutanen da abin ya shafa na daga cikin talakawan da ke zaune kusa da tumbin shara, inda suke dogaro da tattara shara don rayuwa. Wannan ya sake jaddada matsalar tsaro da talauci a irin waɗannan yankuna.
Gwamnati ta ce ta fara bincike domin gano dalilin rugujewar, tare da duba yiwuwar sakaci daga masu kula da wurin, yayin da iyalan waɗanda abin ya shafa ke jiran samun labari kan makomar ‘yan uwansu.