Dakarun Syrian Democratic Forces (SDF) sun janye daga wasu yankunan birnin Aleppo na ƙasar Syria, bayan fafatawar da ta barke tsakaninsu da wasu ƙungiyoyin da ke adawa da su, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Rahotanni daga yankin sun ce gumurzun ya ɗauki kwanaki ana yi, inda aka yi amfani da manyan makamai a wasu sassan birnin, lamarin da ya jefa fararen hula cikin fargaba tare da tilasta wa wasu barin gidajensu.
Majiyoyi sun bayyana cewa janyewar ta SDF ta zo ne domin rage asarar rayuka da kuma kauce wa ƙarin faɗa a cikin birnin, yayin da dakarun gwamnatin Syria da wasu ƙungiyoyi ke ƙoƙarin ƙarfafa ikonsu a yankin.
Kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun ce rikicin ya ƙara tsananta halin da fararen hula ke ciki, musamman mata da yara, inda ake samun ƙarancin abinci, ruwa da magunguna sakamakon tsananin faɗa.
A halin yanzu, ana sa ido kan yadda lamarin zai kaya, yayin da ake fargabar cewa rikicin na iya sake barkewa idan ba a samu fahimta tsakanin ɓangarorin da ke rikici ba.