Shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte ya ce ya gana da Shugaba Trump na AMurka kan halin da ake ciki a Greenland da kuma yankin.
Cikin wani sao da ya wallafa a shafinsa na X, jim kaan bayan ganawar, Rutte ya ce ''Za mu ci gaba da aiki kan haka, kuma za mu sake ganawa a birnin Davos cikin mako mai zuwa.''Trump zai halarci taron Duniya kan tattalin arziki da za a yi a birnin Davos na ƙasar Switzerland, inda shugabannin ƙasashen Faransa da Jamus da Netherland da Finland za su halarta.