Ɗan fafutukar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya koma Najeriya a jiya, ranar Litinin bayan shafe kusan shekaru biyar yana gudun hijira a Jamhuriyar Benin.
Komawarsa na zuwa ne kusan shekaru huɗu bayan samamen da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kai masa a gidansa da ke Ibadan a shekarar 2021, lamarin da ya tilasta masa tserewa daga ƙasar.Rahotanni sun ce Sunday Igboho ya samu damar komawa ne sakamakon afuwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi mi shi, inda aka goge sunansa daga jerin mutanen da hukumomi ke nema ruwa a jallo.
Wannan afuwa ta biyo bayan shiga tsakani da wasu daga cikin manyan sarakunan yankin kudu maso yammacin Najeriya suka yi, waɗanda suka buƙaci gwamnati ta sassauta matsayinta domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Har zuwa yanzu, gwamnati ba ta fitar da cikakken bayani kan sharuddan afuwar da aka ba shi ba.