Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta ja ragamar gwamnatin Venezuela har zuwa lokacin da al'amura za su daidaita tare da miƙa mulki ga gwamnatin da za a kafa.
Da safiyar yau Asabar ne Trump ya sanar da kama shugaban Venezuela Nicolas Maduro da mai ɗakinsa a wani ''mummunan'' hari da Amurka ta kai ƙasar.Kawo yanzu dai bayanai na cewa Mista Maduro na New York inda zai fuskanci shari'a kan zargen-zargen safarar miyagun ƙwayoyi.