Trump Ya Hana Man Fetur da Kudin Venezuela Isa Cuba, Ya Bukaci Sabuwar Yarjejeniya

 Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ba zai sake bari man fetur ko kuɗaɗen Venezuela su ci gaba da zuwa ƙasar Cuba ba, yana mai cewa dole ne a cimma wata sabuwar yarjejeniya kafin hakan ya ci gaba.

Amurka

Trump ya yi wannan jawabi ne yayin wani taro, inda ya zargi gwamnatocin Venezuela da Cuba da cin gajiyar juna ta hanyoyin da ke cutar da muradun Amurka. Ya ce Amurka ba za ta lamunci duk wata mu’amala da za ta ƙarfafa gwamnatocin da yake kira “marasa bin doka da oda” ba.

A cewarsa, Venezuela na taimaka wa Cuba ne ta hanyar bai wa ƙasar man fetur da kuɗaɗe duk da halin takunkuman tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata, lamarin da Trump ya ce dole ne a dakatar da shi matuƙa.

Masana harkokin siyasa sun ce wannan mataki na iya ƙara tsananta matsin tattalin arziki a Cuba, wadda ke fama da matsalar makamashi da tsadar rayuwa, yayin da Venezuela ma ke fama da matsalolin tattalin arziki da takunkumi daga ƙasashen yamma.

Har yanzu dai ba a ji martani kai tsaye daga gwamnatocin Havana da Caracas ba, amma ana sa ran wannan mataki zai ƙara rura wutar rikici tsakanin Amurka da ƙasashen Latin Amurka.

Post a Comment

Previous Post Next Post