Zamani ya hana ɗan'Adam Auratayya

Ban jima da haɗuwa da mutumin da ke da aure da yawa ba, kuma shi kullum a haka yake,'' kamar yadda ta yi bayani.

''Ina son sanin: Me ya sa muka taƙaita da aure da mutum guda a al'ummarmu''?

Hanya ɗaya ta fahimtar hanyar juyin halittar mu ita ce ta nazarin makusantan danginmu na farko da kuma dabarun haihuwarsu.

Goggon birrai kan yi mata da yawa - inda za ka samu biri guda da mata masu yawa,'' in ji Dakta Kit Opie, masanin ilimin yadda halittu suka faro a Jami'ar Bristol a Birtaniya

"Don haka ƴaƴan da ke cikin garken duk goggon biri guda ne mahaifinsu, amma mata daban-daban da ke cikin garken ne suka haifo su.

Amma wannan ba dabarar haihuwa ba ce mai inganci, in ji Dokta Opie, saboda yana haifar da yawan mutuwar jarirai.

Post a Comment

Previous Post Next Post