Al’ummar ƙauyen Kasuwan Daji da ke jihar Neja sun zama na baya-bayan nan da suka fuskanci cin zarafin ƴanbindiga, waɗanda suka kwashe kimanin shekara 10 suna kai farmaki a ƙauyuƙan arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya.
Wani ɗanjarida a jihar Neja ya shaida wa BBC cewa "Ƴanbindigar sun shiga garin a kan babura ɗauke da makamai, inda suka tattara mutane kuma daga baya suka riƙa bi suna masu yankar rago, wasu kuma suka harbe su. Wanda kawo yanzu an tattara gawarwaki aƙalla 42.''Wannan na zuwa ne ƙasa da wata biyu da wasu ƴanbindiga suka sace ɗalibai da malamai sama da 200 a ƙauyen Papiri da ke jihar ta Neja, lamarin da ya tayar da hankulan al’umma.
A baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaddamar da hare-hare kan wasu yankuna na arewa maso yammacin Najeriya da sunan murƙushe ayyukan ƴanbindigar.
Sai dai babu wani bayani da ya iya tabbatar da cewa harin na Amurka ya kashe ko illata irin waɗannan ƴanbindiga da ke kai hare-hare cikin ƙauyuka, suna kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
A wani saƙo da rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Neja ta fitar, ta tabbatar da harin na ranar Asabar, tare da bayyana cewa ‘an kashe mutum fiye da 30’ a ƙauyen na Kasuwan-Daji da ke yankin Demo a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar.
Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane da ba a tantance yawan su ba, tare da ƙona kasuwar bayan sun kwashi kayan abinci da sauran kayayyaki.