Nicolas Maduro Moros shi ne Shugaban Ƙasar Venezuela, muƙamin da ya fara riƙewa tun shekarar 2013 bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Hugo Chávez.
An haifi Maduro a ranar 23 ga Nuwamba, 1962, a birnin Caracas, babban birnin Venezuela. Kafin shigarsa harkar siyasa a matakin ƙasa, ya yi aiki a matsayin direban bas, sannan ya shiga ƙungiyoyin ƙwadago, inda nan ne ya fara fitowa fili a harkar gwagwarmayar kare haƙƙin ma’aikata.
Maduro ya ƙara shahara ne lokacin da ya zama amintaccen makusanci ga Hugo Chávez. A gwamnatin Chávez, ya riƙe mukamin Ministan Harkokin Waje daga 2006 zuwa 2013, sannan daga baya aka naɗa shi Mataimakin Shugaban Ƙasa. Bayan rasuwar Chávez, Maduro ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen da ya janyo cece-kuce, inda aka sanar da shi a matsayin sabon shugaban Venezuela.
A zamanin mulkinsa, ƙasar Venezuela ta fuskanci mummunan matsin tattalin arziki, ciki har da hauhawar farashi mai tsanani, ƙarancin abinci da magunguna, rushewar ayyukan gwamnati da kuma ƙauracewar ‘yan ƙasa miliyoyi zuwa wasu ƙasashe. Gwamnatin Maduro na danganta wannan hali da takunkumin tattalin arziki da Amurka da kawayenta suka kakaba, yayin da masu suka ke zargin gwamnati da cin hanci, rashin kyakkyawan shugabanci da danniya.
Mulkin Maduro ya sha fuskantar kalubale da suka daga jam’iyyun adawa, inda ake zarginsa da murde zaɓe, tsare ‘yan adawa, da tauye ‘yancin faɗin albarkacin baki. Duk da haka, yana samun goyon bayan wasu ƙasashe kamar Rasha, China, Iran da Cuba, waɗanda ke kallonsa a matsayin abokin hulɗa a siyasance.
Duk da matsin lamba daga cikin gida da na ƙasashen waje, Nicolás Maduro na ci gaba da riƙe madafun iko a Venezuela, inda yake da cikakken iko kan hukumomin tsaro da manyan cibiyoyin gwamnati, lamarin da ya sa har yanzu yake kan karagar mulki.