Shaikhul Islami yana magana a kan Ahlus Sunna masu sabani a tsakaninsu, amma kuma sai a samu da yawa daga cikinsu suna afkawa cikin son rai da Ta'assubanci da Kungiyanci, sai ya ce:
يغضبون
على من خالفهم، وإن كان مجتهدا معذورا لا يغضب الله عليه، ويرضون عمن يوافقهم، وإن
كان جاهلا سيئ القصد، ليس له علم ولا حسن قصد، فيفضي هذا إلى أن يحمدوا من لم
يحمده الله ورسوله. ويذموا من لم يذمه الله ورسوله. وتصير موالاتهم ومعاداتهم على
أهواء أنفسهم لا على دين الله ورسوله.
منهاج
السنة النبوية (5/ 255)
"Suna fushi da wanda ya saba musu ko da ya kasance
Mujtahidi ne mai uzuri wanda Allah bai yi fushi da shi ba, suna yarda da wanda
ya bi ra'ayinsu ko da ya kasance jahili mai mummunar manufa, wanda ba shi da
ilimi ba shi da kyakkyawar manufa, wannan sai ya kai su ga yabon wanda Allah da
Manzonsa ba su yabe shi ba, kuma su zargi wanda Allah da Manzonsa ba su zarge
shi ba, sai soyayyarsu da gabarsu ta kasance a kan bin son zuciyoyinsu ba a kan
Addinin Allah da Manzonsa ba".
Abin nufi a nan shi ne; bai kamata ka sanya ma'aunin soyayya da
kiyayya ya zama shi ne bin ra'ayinka da kungiyarka ba. Kawai ma'aunin soyayya
shi ne Imani da jin tsoron Allah. Haka kuma ma'aunin kiyayya shi ne munafurci
da fajirci.
Duk wanda ya kasance Mumini mai jin tsoron Allah, musamman mai
ilimi to wajibi ne ka so shi ko ba a kungiyarka yake ba. Wanda kuma ya zama
Fajiri ba za ka so shi kamar mai tsoron Allah ba, ko da kuwa dan kungiyarka ne.
In muka yi haka sai mu yaki Kungiyanci a tsakaninmu mu Ahlus Sunna.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani