Bayan Shugaban Fastoci (patriarch) ya iso filin taro ya zauna, Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya gaishe shi, har ya tambaye shi yaya iyali, yaya yara?
Nan da nan sai wurin ya kaure da inkari gare shi. Sai yake
tambayarsu menene aibi a maganata?
Sai Paparoma ya ce: Ai su wadannan muna tsarkake su daga mata
da 'ya'ya, ba sa aure.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Abin mamaki, kuna
girmama danganta ma wannan mutumi mace da d'a, kuna tsarkake shi daga mace da
d'a, amma ba ku girmama hakan ga Allah, kuna jingina masa mata da d'a?!
Allah wadai da wannan wautar tunani.
Kawai sai jikinsu ya yi sanyi, suka rasa ta cewa.
Sai Paparoma ya ce wa Shugaban Fastoci (patriarch): Me kake
gani game da wannan Shaidani?
*(Ya gama tsinka su kam ai dole su ce masa Shaidani 😂)
Sai Shugaban Fastoci (patriarch) ya ce: Ai kawai ka gama
sauraron bukatarsa ka sallame shi. A yi sauri a fitar da shi daga kasarka a
yau, don ina tsoron zai zama fitina ga Kiristoci da barazana ga Addinin
Kiristanci.
Ai kuwa haka aka yi, aka tanadi amsar wasikar Sarki Adhudud
Daula, aka tanadi kyaututtuka aka hada shi da su zuwa ga Adhudud Daula. Aka
gaggauta sallamar Alkali Abubakar Al-Baqillaniy, aka hada shi da fursunonin
yaki Musulmai. Aka yi masa rakiya da rundunar Soja don su ba shi tsaro a kan
hanya, har sai ya shiga yankin kasar Musulmai.
*A nan muka zo karshen wannar kissa da muka gabatar da ita a
madadin taya Kiristoci murnan Bikin Kirsimeti. A maimakon mu taya su murna sai
dai mu nuna musu bacin Addinin nasu.
Ga littatafan da aka kawo wannar kissa, imma gaba dayanta ko
kuma yanki daga cikinta:
1- تاريخ بغداد = للخطيب البغدادي (المتوفى:
463هـ)
2- ترتيب المدارك وتقريب المسالك = للقاضي
عياض (المتوفى: 544هـ)
3- الأنساب = للسمعاني (المتوفى: 562هـ)
4- تبيين كذب المفتري فيما نسب إلى الإمام أبي
الحسن الأشعري = لابن عساكر (المتوفى: 571هـ)
5- المنتظم في تاريخ الأمم والملوك = لابن
الجوزي (المتوفى: 597هـ)
6- عيون المناظرات = للسكوني (المتوفى: 717هـ)
7- سير أعلام النبلاء = للذهبي (المتوفى :
748هـ)
8- البداية والنهاية = لابن كثير (المتوفى:
774هـ)
*Mu hadu a kissar Fitinar ra'ayin halittar Alkur'ani, wacce aka
fitini Imamu Ahlis Sunnati wal Jama'a, Imamu Ahmad bn Hanbal da ita, da sauran
Malaman Sunna.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani