Sau da yawa za ka ji fitinu da sabani na rabuwar kai yana faruwa a tsakanin Ahlus Sunna a garuruwanmu, amma in ka duba sai ka ga an makale ne ma wasu mas'alolin Ijtihadi, (wadanda za a iya yin sabani a kansu kuma a zauna lafiya). Wasu ma a galibi mustahabban Sallah ne. Kamar mas'alar Jiyarwa, Rike sanda a huduba, Sallama biyu, Dora hanaye a kan kirji, Jilsatul Istiraha, Tahajjudi, da ire - iren wadannan mas'alolin da suke mas'aloli ne na ijihadi a bisa Ijma'in Malaman Muslunci. Amma abin takaici sai ka ga an fake da wadannan ana ta da rigima, ana rabuwa kungiya - kungiya. Wasu su kira kansu 'Yan Salafiyya, su ware daga Izala, Izalar kuma ta kasu kashi 2, alhali duk wanda Tushensa na daukan Addini ya zama shi ne Al- Qur'ani da Sunna da Ijma'in magabata, sa'annan bai saba ma Ahlus Sunna a kan wani Tushe daga cikin tushen Sunna ba, kuma ya nisanci bidi'a, to shi Ahlus Sunna ne Dan Salafiyya.
Abin tambaya: Don me ya sa ake rarrabuwa kungiya - kungiya
saboda mas'alolin ijtihadi, alhali ba su kai su raba kai ba?
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
الاجتهاد
السائغ لا يبلغ مبلغ الفتنة والفرقة إلا مع البغى، لا لمجرد الاجتهاد،
كما
قال تعالى: (وما اختلف الذين أوتوا الكتاب إلا من بعد ما جاءهم العلم بغيا بينهم)
[سورة آل عمران 19]، وقال: (إن الذبن فرقوا دينهم وكانوا شيعا لست منهم في شيء)
[سورة الأنعام 159]، وقال: (ولاتكونوا كالذين تفرقوا واختلفوا من بعد ما جاءهم
البينات) [سورة آل عمران 105].
فلا
يكون فتنة وفرقة مع وجود الاجتهاد السائغ بل مع نوع بغى
"Ijtihadi a mas'alolin da ake iya yin ijtihadi a cikinsu
(kananan mas'alolin Addini na Aqida da na Fiqhu), ba ya kai wa ga matsayin
fitina da rabuwar kai, sai dai in akwai zalunci a tare da sabanin, ba dai kawai
sabani a ijtihadin ba. Kamar yadda Allah ya ce:
(وما اختلف الذين أوتوا الكتاب إلا من بعد
ما جاءهم العلم بغيا بينهم)
"Wadanda aka ba su littafi (Yahudawa da Nasara) ba su yi
sabani ba sai bayan ilmi ya zo musu, a dalilin ZALUNCI a tsakaninsu".
Kuma du ya ce:
(إن الذبن فرقوا دينهم وكانوا شيعا لست منهم
في شيء)
"Lallai wadanda suka rarraba addininsu suka zama kungiya -
kungiya, ba ka tare da su a komai (Annabi (saw) ya barranta da su a
komai)".
Kuma du ya ce:
(ولاتكونوا كالذين تفرقوا واختلفوا من بعد
ما جاءهم البينات)
"Kada ku zama kamar wadanda suka rarrabu suka yi sabani
bayan hujjoji da shiriya sun zo musu (wato Yahudawa da Nasara kenan)".
Don haka fitina da rabuwar kai (a tsakanin Ahlus Sunnah) ba sa
kasancewa a tare da yin Ijtihadin da ya halatta, (a mas'alolin da za a iya yin
Ijtihadi a cikinsu), a'a, sai dai a samu fitinar da rabuwar kan a dalilin nau'i
na zalunci".
Duba Al- listiqama 1/ 31.
Don haka ashe fitina da rabuwan kan ba kawai a dalilin sabani a
mas'alolin Ijtihadi ba ne, a'a, a dalilin zalunci ne na magana ko na aiki,
saboda wata manufa ta zahiri ko ta cikin zuciya.
Abin lura:
1. Ahlus Sunna shi ne duk wanda ya yarda da Al- Qur'ani da
Sunna da Ijma'i a matsayin tushen daukan Addini, kuma bai saba da Salaf
(magabata) a kan wani Asali daga cikin Asalin Sunna ba. (manyan mas'alolin
Sunna), kuma ya nisanci bidi'a. To wannan shi ne Ahlus Sunna kuma Dan
Salafiyya, ko da kuwa babu wanda ya taba kiransa da sunan Salafiyya.
2. Bai halatta Ahlus Sunna suna fitina a tsakaninsu ba, su
rinka rabuwa kungiya - kungiya a dalilin kananan mas'alolin Addini ba, wadanda
za a iya yin ijtihadi a cikinsu.
3. Duk lokacin da ka ga ana fitina, an rabu a kan mas'alolin
Ijtihadi, to ko shakka babu, ba kawai sabani a kan mas'alolin ba ne ya janyo
rabuwar, a'a, dole akwai zalunci daga daya bangare, ko daga guda bangarorin.
4. Zaluncin nan (Bagyu) shi ne wuce iyakan Shari'a da baki ko
da aiki, ko kin gaskiya saboda wata bukata.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani