Ibnu Taimiyya Mu'ujizar Annabi (SAW) Ne

Wato Ibnu Taimiyya wata Aya ce daga cikin Ayoyin Allah. Shi ya sa hatta Sufaye ma akwai waɗanda Fiɗira ta tilasta su suka so Ibnu Taimiyya, suka yabe shi. Wannan kuwa tun a zamaninsa ne. Shi ya sa a lokacin da ya mutu, dubban Sufaye ne suka yi dandazo wajen yi masa Sallah, da raka shi maƙabarta, da yin tabarruki da shi. Suka kai shi maƙabartar Sufaye. Suka yi ta rera waƙoƙi na ta'aziyya, wasu waƙoƙin har akwai guluwwi a cikinsu.

Ko a wannan zamani akwai waɗanda Fiɗira take tilasta musu faɗin gaskiya a kansa, da kore tuhumar da maƙiyansa suke yi masa. Kamar Sharif Ibrahim Saleh, wanda ya tabbatar da cewa: Ibnu Taimiyya babban Malami ne. Ya kuma ƙaryata alaƙar ƴan ta'adda da shi. Haka Ali Jumu'a ma. Da sauransu, suna da yawa.

Kuma wannan gaskiya ne. Duk wanda ya san Ibnu Taimiyya to dole sai ya so shi, saboda Allah ya yi masa baiwa masu yawa, da kyawawan halaye, da ilimi, da kaifin kwakwalwa, da jihadi, da ibada da son alheri wa Musulmai.

Saboda zurfin iliminsa, da zurfinsa a ilmummuka na hankali, babban Malamin India Shibliy al-Nu'umaniy, ya ce: tun da ya karanta littatafan Ibnu Taimiyya, sai al-Raziy da al-Gazzaliy suka faɗi a idonsa. Ma'ana; suka dena yi masa kwarjini. Saboda a da suna matuƙar birge shi, amma tun da ya karanta Ibnu Taimiyya sai ya ga ashe nasu nafila ne.

Haka Dr. Bashar Auwad ma, masanin ilimin "Rijal", wato maruwaita Hadisi, shi kuma har rantsuwa ya yi, ya ce: ya karanta dubban tarjamomin maruwaita, amma tun bayan Sahabbai, bai gani ba, kuma bai ji labarin wani mutum a duniya kamar Ibnu Taimiyya ba, a jarumtaka, da Jihadi, da ilimi.

Wasu kuma da yawa suna jera shi a sahu ɗaya da "al-A'immatul Arba'a", wajen imamanci a Addini.

Wato mutum ne da Allah ya masa baiwa masu yawa. Halin da ake ciki a yanzu, a Jami'o'in Turawa sun duƙufa wajen karanta rayuwarsa da littatafansa, don sun gane cewa; a Muslunci ba a yi mai ilmummukan hankali (العقليات) irinsa ba.

Kuma wani abin mamaki, shi malami ne da a kowane zamani shi ne a gaba. Shi ya sa Dr. Tha'ir al-Hallaq ya ce: wannan zamanin da muke ciki zamanin Ibnu Taimiyya ne. Saboda yadda za ka samu warwaran matsalolin zamani a cikin littatafansa, da yadda yake tasiri wa masu kawo gyara cikin al'umma, da jaddada Addini.

Don haka samun Ibnu Taimiyya a cikin al'ummar Annabi (saw) yana daga cikin Mu'ujizozin Annabi (saw). Saboda mutum irinsa, tun da ya yi imani da Annabi (saw), ya zama a gaba wajen kira ga ɗa'a wa Manzon Allah (saw), da ba da kariya ga Sunnarsa, da Addinin da ya zo da shi, to lallai gaskiya ne, Annabi Muhammad (saw) Manzon Allah ne, babu kwokwanto. Ma'ana; da a ce: Annabi (saw) ba Manzon Allah ba ne, da mutum irin Ibnu Taimiyya bai yi imani da shi ba.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post