Me Ya Raba Kan Al'ummar Musulmi?

Mutane da yawa suna yawan magana a kan rabuwar kan Musulmi, suna koka cewa; Musulmai sun rabu gida - gida, akwai 'Yan Izala, 'Yan Darika har an samu 'Yan Shi'a da Khawarijawa, irin 'Yan Boko Haram da makamantansu.

Abin mamaki, cikin masu korafi a kan rarrabuwar Musulmi, har da 'Yan Boko Aqida. Sai ka ji yana korafi, yana zagin Musulmai, yana siffanta su da munanan siffofi, saboda sun rabu kungiyoyi. Sai ka ji yana cewa: Ni kawai Musulmi ne, ba ruwana da kowace kungiya. Ai kowace kungiya tsarkake kanta take yi tana cewa; ita ce 'yar Aljanna. Yana wadannan surutai alhali yana cikin manyan masu raba kan Musulmai. Saboda babu wani sababi na rabuwar kai face yana aikatawa, kuma yana kira ga aikatawan.

Daga cikin wadannan sabuba akwai:

1- Sabon Allah: Lallai lokacin da al'umma ta yi dumu-dumu cikin sabon Allah to dole za a rasa soyayya a tsakaninsu, sai rarrabuwa ya afku a cikinsu. Saboda Imani da kyawawan aiyuka da da'a ma Allah su suke sa Allah ya sanya soyayya tsakanin bayi. Allah ya ce:

{إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَيَجْعَلُ لَهُمُ الرَّحْمَنُ وُدًّا} [مريم: 96]

"Lallai wadanda suka yi imani, suka aikata aiyuka na gari Allah Mai rahma zai sa a so su".

2- Bidi'a: Lallai kirkirar Bidi'a a cikin Addini da bin tafarkin Bidi'a, da saba tafarkin Manzon Allah (saw) da Sahabbansa yana lazimta rarrabuwar al'umma. Hakan ya tabbata a Hadisin da Annabi (saw) ya ba da labarin rarrabuwar al'ummarsa kashi 73, wanda rabuwa da tafarkin Sunnar Annabi (saw) shi ya janyo wannan rarrabuwar.

3- Munanan halaye da munanan dabi'u: Duk lokacin da mutane suka zama marasa mutunci a tsakaninsu, suna mu'amalantar juna da munanan halaye da miyagun dabi'u, to dole su rarrabu kashi - kashi. Wannan ya sa Annabi (saw) ya hane mu ga munanan halaye inda ya ce:

«إياكم والظن، فإن الظن أكذب الحديث، ولا تحسسوا، ولا تجسسوا، ولا تناجشوا، ولا تحاسدوا، ولا تباغضوا، ولا تدابروا، وكونوا عباد الله إخوانا»

صحيح البخاري (8/ 19)، صحيح مسلم (4/ 1985)

"Kar ku yi mummunan zato, kar ku yi sa ido, kar ku yi tajassusi, kar ku yi najashu a kasuwanci, kar ku yi hasada, kar ku yi kiyayya, kar ku juya baya wa juna, kar wani ya yi ciniki a kan cinikin dan uwansa, kar ku yi gasa a junanku".

To in ka duba wadannan duka za ka ga 'Yan Boko Aqida sun fi kowa sabon Allah da halasta saba masa, da yakar masu hani a kan aikata sabo da sunan 'yanci. Sun fi kowa Bidi'a da dauko tunanin 'Yan Bidi'ar, da kare su. Haka sun fi kowa munanan halaye da cin mutuncin mutane. A ko'ina wadannan su ne manyan halayensu.

Saboda haka in da gaske muke yi, muna son hadin kan Musulmi, to sai mun nisanci sabon Allah ta kowace fiska, mun nisanci Bidi'ao'in da aka shigo da su cikin Addini, Bidi'o'i na Aqidu da na aiki, kuma sai mun siffantu da kyawawan halaye da dabi'u managarta da kiyaye mutuncin mutane.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post