Ta Yaya Ake Gane Malami?

Tushen matsalarmu shi ne, al'ummarmu ba ta san miye ilimi ba, balle ta san su waye ma'abota ilimi, cikin Malamai da Ɗaliban ilimin. Wannan ya sa kowane mai neman suna ko neman ɗaukaka ko wata manufa ta daban sai ya saka rigar malumta yana neman abin Duniya da ita.

Shi Ilimi yana da sharaɗi ta ɓangarori guda huɗu:

1- Sharaɗi ta ɓangaren Ibada:

Wannan shi ne sharaɗi wajen tabbatar da Ikhlasi da yinsa don Allah da neman yardarsa, da kuma yin aiki da ilimin, da yin ibada da shi, da karantar da shi da kira zuwa gare shi.

Dalili a kan wannan sharaɗi shi ne faɗin Allah Maɗaukaki:

{كُونُوا رَبَّانِيِّينَ بِمَا كُنْتُمْ تُعَلِّمُونَ الْكِتَابَ وَبِمَا كُنْتُمْ تَدْرُسُونَ} [آل عمران: 79]

"Ku zamo Na-Allah saboda abin da kuka kasance kuna yi na koyar da littafi, kuma kuke yin darasinsa".

Ma'ana; mutum ya zama Na-Allah mai Ikhlasi, da aiki da ilimin da yake koyarwa.

2- Sharaɗi ta ɓangaren Akhlaƙ da halayen ilimi:

Wannan shi ne sharaɗi ta ɓangaren sanin halayen ilimi wajen koyonsa, da kuma wajen isar da shi. Daga cikin manyan halayen ilimi akwai:

1) Girmama Maganar Allah da Maganar Manzonsa (saw), da gabatar da su a kan maganar kowa.

2) Nisantar yin magana ba tare da ilimi ba.

3) Rashin ɓoye ilimi.

d.s.

Dalili a kan wannan sharaɗi shi ne faɗin Allah Maɗaukaki:

{وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِنْ عِنْدِ رَبِّنَا} [آل عمران: 7]

"Tabbatattu a cikin ilimi, cewa suke yi: Mun yi imani da shi (Ayoyi masu rikitarwa), dukansu daga wajen Ubangijinmu suke".

A wani wajen kuma ya ce:

{لَكِنِ الرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ مِنْهُمْ وَالْمُؤْمِنُونَ يُؤْمِنُونَ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ} [النساء: 162]

"Tabbatattu a cikin ilimi daga cikinsu (Ahlul Kitabi), da Muminai suna yin imani da abin da Allah ya saukar maka, da abin da aka saukar kafinka".

Ka ga kenan, Malamai ba sa karan tsaye wa maganar Allah da ta Manzonsa (saw).

3- Sharaɗi ta ɓangaren Manhaji da hanyar ilimi:

Wannan shi ne sharaɗi ta ɓangaren sanin hanyar Malamai wajen koyon ilimi da isar da shi. Ta hanyar yin amfani da yaren ilimi da tsarinsa, kamar yadda yake a wajen Malamai. Misali: mutum ya zo yana karan tsaye ma Aƙida ba tare da san yaren Malaman Aƙida da tsarinsu ba, haka ilimin Hadisi, za ka ga kowa yana hawan ƙawara wa Hadisi ba tare da sanin yare da tsarin Malaman Hadisi ba. Haka yaren ilimin Tafsiri da tsarinsa, da yaren ilimin Fiƙhu da Usul da tsarinsu, d.s.

4- Sharaɗi ta ɓangaren Fiƙhu da fahimta:

Wannan sharaɗi shi ne ta ɓangaren fahimtar dalilan Shari'a da mas'alolinta, da fahimtar maganganun Malamai da tsari da Manhajin manyan Malamai magabata da na bayansu, musamman masu Tahƙiƙi a cikinsu.

Bisa wannan tsari ake koyon ilimi. Duk wanda yake so ya zama cikin masu ilimi, waɗanda Allah ya yabe su to sai ya bi wannar hanya.

Da wannan za ka san cewa; daga ka ji mutum yana karan tsaye wa Nassoshin Shari'a, ba ya girmama Maganar Allah da ta Manzonsa (saw), ba ya magana da yaren ilimi, bai fahimci yadda ake mu'amalantar Nassoshi da maganganun Malamai ba, to ka sani kawai wannan ɗan dagaji ne, ba shi da alaƙa da ilimi, kawai wata manufarsa yake so ya cimma na neman abin Duniya.

Don haka da zaran ka ga wani yana jayayya da Ayar Alkur'ani ko Hadisi tabbatacce, to wanke hanunka daga gare shi, kar ka taɓa ɗaukarsa a matsayin Malami, ko da an buga tambari a goshinsa cewa shi Malami ne.

Saboda haka da samuwar irin waɗannan sharuɗa ake iya gane Malami daga ƴan shisshigi masu tsoma baki a abin da ba hanyarsu ce ba, masu shiga gonar da ba tasu ba.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post