Rukuni na biyu a cikin rukunai biyar na Mu'utazilanci shi ne Adalci.
To miye ma'anar adalci a wajen Mu'utazilawa?
Ga nan bujumin Malami a cikinsu, zai ba mu amsa inda ya ce:
"فإن
قيل: فأخبرني عن العدل ما هو؟
قيل له: هو العلم بتنزيه الله عز وجل عن كل
قبيح، وأن أفعاله كلها حسنة.
وتفسير ذلك؛ أن تعلم أن جميع أفعال العباد
من الظلم والجور وغيرهما لا يجوز أن يكون من خلقه. ومن أضاف ذلك إليه فقد نسب إليه
الظلم والسفه، وخرج من القول بالعدل...
وتعلم تعالى أنه لا يريد المعاصي ولا
يشاؤها...".
الأصول الخمسة للقاضي عبد الجبار المعتزلي
(ص: ٦٩)
Ka ga ƙarara, a fili, Babban Malamin Mu'utazilawan ya ce:
ma'anar Adalcin Allah shi ne; a tsarkake Allah daga munanan abubuwa. Fassarar
haka shi ne:
"Ka san cewa; dukkan aiyukan bayi na zalunci da danne
haƙƙi da wasunsu, bai halasta su kasance halittar Allah ba. Duk wanda ya
danganta halittarsu ga Allah to ya danganta masa zalunci da wauta (rashin
hikima), ya fita daga Aƙidar Adalci...
Kuma ka san cewa; Allah Maɗaukaki ba ya nufin faruwar aiyukan
saɓo, kuma ba ya ganin daman faruwarsu...".
Wannan shi ne ra'ayinsu.
Alhali Allah ya ce:
﴿وَٱللَّهُ
خَلَقَكُمۡ وَمَا تَعۡمَلُونَ ٩٦﴾ [الصافات ٩٦]
{Kuma Allah ne ya halicce ku, da ma abin da kuke aikatawa}.
Kuma ya ce:
﴿وَمَا
تَشَاۤءُونَ إِلَّاۤ أَن یَشَاۤءَ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِیمًا حَكِیمࣰا﴾
[الإنسان ٣٠]
{Kuma ba za ku ga daman aikata wani abu ba, sai idan Allah ya
ga dama}.
To ka ga wannan ra'ayi nasu, ya ci karo da Alƙur'ani da Sunna.
Da ma su ba ruwansu da Alƙur'ani, balle Hadisi a wannan babin. Sai dai
hankalinsu (son zuciyoyinsu) kawai.
Don haka, idan ka san haƙiƙanin zalunci a Shari'a, to lallai za
ka san cewa; Adalcin Mu'utazilawa na cewa; Allah bai halicci aiyukan bayi ba,
kuma bai ƙaddara su ba, - wai - bayi ne suka halicci aiyukansu da kansu, wannan
shi ne zalunci mafi girma. Saboda zalunci nau'i uku ne:
1- Shirka ma Allah.
2- Zaluntar bawa, da danne masa hakki.
3 - Zaluntar kai, ta hanyar aikata saɓo.
A cikinsu, na farkon - wato shirka ma Allah - shi ne zalunci
mafi girma.
﴿إِنَّ
ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِیمࣱ﴾ [لقمان ١٣]
{Lallai shirka zalunci ne mai girma}
To bisa wannan Adalci nasu, Mu'utazilawa shirka suke yi ma
Allah, shirkan ma mafi munin shirka, wato shirka ma Allah a cikin Rububiyya da
halitta.
To idan Adalcin Mu'utazilawa shi ne cewa; Allah bai halicci
aikin bawa ba, bawa shi ya halicci aikinsa, to wannan sanya ma Allah abokin
tarayya ne a halitta. Wannan kuwa shirka ne a Rububiyya. Ma'ana; Allah ba shi
kaɗai ne mahalicci ba, kowane bawa ma mahalicci ne, shi ne mahaliccin
aiyukansa, shi yake halittarsu da kansa.
To ka ga a fili; wannan shirka ne ma Allah! Kai, shi ne ma
shirka mafi girma kai tsaye, wato shirka a cikin Rububiyya, shirkan da hatta
Mushrikan Makka ba su yi irinsa ba.
Saboda haka Adalcin Mu'utazilawa babu abin da zai koyar da kai
sai zalunci, zaluncin ma mafi girman zalunci.
Don haka duk mai son koyon adalci, to ya koma ga Littafin
Allah, da Sunnar Manzonsa (saw), da Tarihin Khalifofinsa da Sahabbansa. Ba a
ce; mutum ya koma adalcin Mu'utazilawa ba, wanda shi ne ƙololuwar zalunci a
bayan ƙasa.
To yanzu, don Allah, wannan adalcin ne ake so a tallata shi wa
mutane?!
Tir!
***
Hadisan Annabi (saw) su ne Ma'auni
Yarda da Hadisan Annabi (saw) da binsu, shi ya banbance
tsakanin Ahlus Sunna da ƴan bidi'a.
Zai yi wahala ka samu mutum mai amsa sunan Musulmi, amma kuma
ya ce maka bai yarda da Alƙur'ani (a dunƙule) ba.
Amma za ka samu da yawa suna inkarin Hadisai. Imma inkarin
Hadisan duka gaba ɗaya, ko ɓangare. Musamman Hadisan Aƙida, ko Hadisan da suka
shafi rayuwar Annabi (saw), da zamantakewarsa.
Wannan ya sa, Alamar ɗan bidi'a ita ce ƙin Hadisan Annabi
(saw).
Saboda duk wani ɗan bidi'a za ka same shi yana ƙin wasu
Hadisai, yana sukarsu, ko yana ƙaryata su.
Waɗanne Hadisai ne haka?
Su ne Hadisan da suka saɓa son zuciyarsa,
Hadisan da suka saɓa bidi'arsa,
suka saɓa ra'ayoyin shehinsa,
ko ra'ayoyin ƙungiyarsa.
Amma da zaran ka ga mutum ya yarda da Hadisan Annabi (saw),
ingantattu, to wannan shi ne Ahlus Sunna.
Don haka alamar Ahlus Sunna ita ce bin Hadisan Annabi (saw).
Alamar ƴan bidi'a kuma kishiyar haka.
Mai hankali shi ne wanda ya dauki Duniya a matsayin gada da zai
hau ya tsallaka zuwa ga rayuwa matabbaciya. Allah ya ba mu labarin wani mai
hankali yana wa'azi ga mutanensa inda ya ce:
{يَاقَوْمِ
إِنَّمَا هَذِهِ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا مَتَاعٌ وَإِنَّ الْآخِرَةَ هِيَ دَارُ
الْقَرَارِ} [غافر: 39]
"Ya ku mutane na, lallai ku sani, wannar rayuwar Duniyar
fa dan jin dadi ne kadan, Lahira fa ita ce digan tabbata".
Kowa yana ganin abin da yake faruwa, Duniya za ta yi dadi ta yi
kyau, ta zama abin sha'awa a idon mai kallonta, sai ya karkata gare ta, ya
manta da hikimar halittarsa, ya mayar da manufar rayuwarsa ita ce samun abin
Duniya da jin dadi da sharholiya a cikinta, sai ta gama jan hankalinsa, ya gama
ruduwa da ita, har sai ya yi zaton ya same ta, yana ganin ya gama mallakarta,
kawai sai ya ji gyat, mai yanke jin dadi ta yanke masa jin dadin Duniya, shi
kenan kuma an rabu.
Ya kamata ka zama mai hankali, rayuwa da mutuwa duka masu
wa'azi ne.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani